Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

Mummunan Kisan Mafarauta a Uromi: Bello El-Rufai Ya Nema Ayi Adalci

Published

on

Mohammed Bello El-Rufai, Dan majalisa mai wakiltar jama’ar Kaduna ta Arewa.

Mohammed Bello El-Rufai, Dan majalisa mai wakiltar jama’ar Kaduna ta Arewa a majalisar taraya kuma Shugaban Kwamitin Tsare-Tsare na Bankuna, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan kisan gillan da aka yi wa mafarauta a Uromi, Jihar Edo.

Inda yanuna alhini da takaicin sa kan wadannan mafarauta da cewa an zarge su da laifi, an kai musu hari, sannan aka ƙone su a raye cikin wani mummunan aiki na rashin tausayi.

El-Rufai ya bayyana cewa wannan lamari yana nuna bukatar gaggawa na magance tashin hankali da ake yi tsakanin jama’a da kuma rage son zuciya a cikin al’umma. Ya yi tir da yadda aka aiwatar da “Jungle justice” – wato hukuncin kai tsaye ko hukunci na zalunci da ake aiwatarwa ba tare da bin tsarin doka ba – wanda ke sabawa tsarin shari’a da hakkin ɗan adam. Wanda yake nuna cewa al’umma ko mutane ba za su iya daukar doka a hannunsu ba tare da bin doka ba.

El-Rufai ya kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Edo su dauki matakan gaggawa wajen tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan kisan sun fuskanci hukunci daya dace da aikin da suka aikata.

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙoƙari wajen hana irin wannan mummunan lamari ya sake faruwa a nan gaba. Hakanan ya bayyana cewa zargi ba zai zama hujja ta laifi ba, kuma babu wanda ya cancanci a yi masa hukunci ba tare da shari’a ba.

A ƙarshe Elrufai ya miƙa sakon ta’aziyyar sa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu. Wannan ba abu bane da ya shafi yankin Arewa kadai mummunan al’amari ne da ya shafi kasa baki ɗaya.

Dole ne mu tashi mu yi kokari don kawo karshen wannan hukunci na zalunci da tabbatar da cewa babu wani dan ƙasa, ko daga kabila ko addini, da zai fuskanci irin wannan ta’asa a nan gaba. A cewar Sa.

Copyright © 2024 kaduna Reports.