Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

Rashin Isasshen Tallafi Na Barazana Ga Manyan Makarantun Kaduna – CISDF

Published

on

Kaduna, Najeriya

Gidauniyar Civic Impact for Sustainable Development Foundation (CISDF) ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta kara kaimi wajen ware kudade domin ceto manyan makarantun jihar daga durkushewa.

A cikin wata sanarwa da Gabriel Adinga, Shugaban Sashen Bincike da Kididdiga na gidauniyar, da Waniya Ilu, Shugaban Sashen Gudanarwa Mai Bude Kofa da Cigaban Dorewa, suka fitar, an bayyana cewa duk da karuwar kaso na kasafin kudin ilimi daga 2023 zuwa 2025, manyan makarantun jihar kamar Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya (COE), da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli (NBPZ) na fama da karancin kudade.

Binciken CISDF ya gano cewa:

Kudaden da aka ware wa bangaren ilimi sun karu da 110% tsakanin 2023 da 2025, amma kaso da manyan makarantun suka samu bai kai 25% ba.

A 2023, KASU ta samu 17.6%, COE Gidan Waya ta samu 2.7%, yayin da NBPZ ta samu 2.9% na jimillar kasafin ilimi.

A 2024, kaso na KASU ya ragu zuwa 16.2%, COE ta samu 2.5%, kuma NBPZ ta samu 2.6%.

Babban ayyuka guda biyar mafi tsada a manyan makarantun sun kasa kashi 0% wajen aiwatarwa har zuwa watan Satumba 2024.

Kasafin kudin da aka ware wa manyan makarantun bai taka kara ya karya ba, domin bai iya daukar albashi da ayyukan ci gaba ba.

Wani abin damuwa shi ne yadda gyaran kasafin kudin jihar ke rage adadin kudaden da ake ware wa bangaren ilimi. A shekarar 2023, an rage kasafin daga 28.0% zuwa 27.6% sannan daga 25.2% zuwa 19.6%, lamarin da ya rage damar samun kudade a manyan makarantun.

Shawarwarin da CISDF ta bayar

Gidauniyar ta bukaci gwamnatin jihar da ta dauki matakan gaggawa domin dakile wannan matsala. Daga cikin shawarwarin da suka bayar:

A ci gaba da bunkasa kasafin ilimi don tabbatar da cewa matsalolin da ake fuskanta sun samu magani.

Gwamnatin jiha ta daidaita rabon kudaden ilimi domin tabbatar da cewa manyan makarantu sun samu isasshen tallafi.

A daina rage kasafin ilimi a lokacin da ake sake duba kasafin kudi, domin hakan yana shafar ci gaban manyan makarantu.

A saki kudaden da aka ware wa manyan makarantu akan lokaci, domin gujewa tsaikon biyan albashi da aiwatar da ayyukan ci gaba.

Manyan makarantun su inganta yadda suke amfani da kudaden da aka basu tare da nemo hanyoyin samun karin kudin shiga.

A binciki dalilan da suka hana aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa domin bullo da hanyoyin magance su.

A tabbatar da cewa manyan ayyukan da suka fi muhimmanci sun samu kudaden da za su kammalu akan lokaci.

Gwamnatin jiha ta karfafa hanyoyin samun kudin shiga a manyan makarantu domin rage dogaro ga kasafin kudi kadai.

A duba hanyoyin da aka bi a 2024 don samun karin kudin shiga domin tabbatar da cigaba da nasara.

A tabbatar da cewa duk wata gyara da za a yi a kasafin kudi bai shafi ayyukan ci gaba a manyan makarantu ba.

Rashin Ingantaccen Tallafi na Barazana ga Makomar Dalibai

Gidauniyar CISDF ta bayyana cewa idan aka ci gaba da sakaci, ingancin ilimi a Kaduna zai ci gaba da tabarbarewa, lamarin da ka iya haifar da illa ga makomar dalibai da cigaban jihar gaba daya.

Gidauniyar ta bukaci gwamnan jihar Mallam Uba Sani da ya dauki wannan batu da muhimmanci, domin idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, tabarbarewar ilimi a jihar na iya zama barazana ga cigaban Kaduna a nan gaba.

Dole ne a hada kai domin tabbatar da cewa manyan makarantun Jihar Kaduna sun samu isassun kudade don samar da ingantaccen ilimi ga matasa, wadanda su ne ginshikin makomar jihar.

Domin samun cikakken rahoton kasafin kudin ilimi, za a iya tuntubarmu ta civicimpact4sd@gmail.com.

Za mu ci gaba da bibiyar wannan batu da kuma jin martanin gwamnatin jiha kan wannan kiran.

Copyright © 2024 kaduna Reports.