A ci gaba da kokarinta na tallafawa al’ummarta yayin azumin Ramadan, Hon. Munira Suleiman Tanimu, mamba a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar Mazaɓar Lere East kuma Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, ta shirya liyafar bude baki tare da al’ummar mazabarta.
Taron, wanda ya gudana a ranar Alhamis, 27 ga Maris, 2025, ya samu halartar Musulmai da Kiristoci, tare da manyan shugabanni daga matakin jiha da na ƙasa. Daga cikin manyan baki da suka halarta akwai: Hon. Abubakar Hassan Nalaraba, mamba a Majalisar Tarayya daga Jihar Nasarawa, Hon. Jafaru Ahmed, shugaban karamar hukumar Lere, wanda ya wakilci Alh. Tasiu Bako Nabawa (Garkuwan Saminaka), Hon. Mathew Gambo Bulus Kaku, tsohon shugaban karamar hukumar Lere, Hon. Abubakar Sadiq Gifted, kakakin majalisar dokokin karamar hukumar Lere da mambobinsa, Sarakunan gargajiya, limamai, fastoci, da shugabannin addini daga yankin.
Dubban al’ummar Lere East da mashawartan siyasa na Hon. Munira.Fiye da mutum 300 ne suka halarci bikin, inda kowannensu ya samu N5,000 a matsayin tallafi daga Hon. Munira domin saukaka musu shagulgulan Sallah da ke tafe.
A cewar Ibrahim Munir, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Hon. Munira ta gode wa mahalarta taron tare da yin addu’a na musamman ga shugabanni da al’ummar Lere East. Ta yi fatan zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban yankin, tare da jaddada muhimmancin taimakon juna da goyon bayan juna a cikin al’umma.
Liyafar ta gudana cikin nasara, inda ta kara karfafa zumunci da hadin kai tsakanin al’umma, tare da nuna muhimmancin taimakon juna musamman a lokacin azumi.