Ministan Tsaro, Mataimakiyar Gwamna Kaduna tare da Chief of Defence.
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ta wakilci Gwamna, Mai Girma Sanata (Dr.) Uba Sani, a matsayin Bako na Musamman a wajen bude horo da samar da kayan aiki ga rukunin farko na jami’ai 800 na Rundunar Ayyuka na Musamman (Special Operation Force) na Rundunar Sojin Najeriya, wanda aka gudanar a Camp Kabala, Jaji.
Da take magana a wajen taron, Dr. Balarabe ta ce” Gwamna Uba Sani ya na bayyana godiyarsa ga dakarun da ke sanye da kaki bisa jajircewarsu da sadaukarwarsu wajen kare rayuka da dukiyoyi a Jihar Kaduna.
Takara da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da marawa jami’an tsaro baya tare da ba su dukkan goyon bayan da suke bukata domin tabbatar da nasarar shirin horon da suke gudanarwa a jihar Kaduna.
A yayin taron, Mataimakiyar Gwamna ta kaddamar da gine-ginen masauki da za a yi amfani da su wajen kwana a lokacin shirin horo na tsawon watanni uku.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da na rundunar soji, ciki har da Ministan Tsaro, Mai Girma Alhaji Mohammed Badaru Abubakar CON, mni; Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa; wakilan shugabannin hukumomin tsaro, kwamishinoni, da manyan jami’an soji.