Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Siyasa

Zamu Dauki Matakin Shari’a Kan Zargin da Elrufa’i Yayi a Kan Mu – Majalisar Dokokin Kaduna

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Mayar Da Martani Ga Zargin El-Rufai, Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Shari’a

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta yi watsi da zarge-zargen da tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya yi a wata hira da ya yi da Freedom Radio Kaduna kwanan nan.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 17 ga Maris, 2025, Majalisar ta mayar da martani kan manyan zarge-zargen da tsohon gwamnan ya yi, tana mai cewa hakan karya ce kuma ba su da tushe.

Zargin Rashin Ilimi Daga Cikin ’Yan Majalisa

El-Rufai ya bayyana cewa membobin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna “babu ilimi kwata-kwata.” A martaninta, Majalisar ta bayyana cewa dukkan mambobinta sun cika ka’idojin cancanta kamar yadda Sashe na 106 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa gyara) ya tanada.

Haka kuma, Majalisar ta jaddada cewa yawancin mambobin Majalisar ta 10 sun rike mukamai a zamanin El-Rufai, don haka kalamansa sun sabawa juna, tunda shi kansa ya yi aiki tare da su a baya.

Zargin Rashin Iko Wajen Bincike

Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa Majalisar ba ta da ikon bincikar gwamnatinsa. A martaninta, Majalisar ta yi watsi da wannan ikirari, tana mai jaddada cewa Sashe na 128 da na 129 na Kundin Tsarin Mulki sun ba ta cikakken iko na gudanar da bincike a kan duk wani lamari da ya shafi huruminta na doka.

Majalisar ta kara da cewa tana aiki ne bisa doka wajen gudanar da bincikenta.

Zargin Cewa Rahoton Kwamitin Bincike An Rubuta Shi Ne Da Kudi

El-Rufai ya kuma zargi cewa rahoton da Kwamitin Bincike na Majalisar ya fitar wani mutum ne ya rubuta bayan an biya shi.

Majalisar ta karyata wannan zargi, tana mai cewa dukkan mambobinta sun cancanci zama ’yan majalisa ta fuskar doka, ilimi da kuma dabi’a.

Ta kuma bayyana cewa rahoton kwamitin binciken yana hannun jama’a, kuma duk kokarin da tsohon gwamnan ya yi na kalubalantar rahoton a kotu ya ci tura.

Majalisar ta ce muddin wata kotu ba ta rushe rahoton ba, to El-Rufai yana nan a matsayin wanda aka zarga da laifuka.

Majalisar ta yi Allah wadai da kalaman tsohon gwamnan da ya kira mambobinta “babu ilimi.” Saboda haka, ta bayyana shirinta na daukar matakin shari’a domin kare mutuncinta da kuma ’yan majalisarta.

Bayani Kan Cire Shugaban KADIRS

Dangane da zargin cewa Kakakin Majalisar ne ya yi tasiri wajen cire tsohon Shugaban Hukumar Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS), Majalisar ta fayyace cewa Kakakin ba shi da iko na nada ko cire wani jami’in gwamnati.

Ta jaddada cewa an bi doka da tsari wajen sauke shugaban KADIRS, don haka duk wata magana da ke cewa Kakakin ne ya sa aka cire shi ba gaskiya ba ce.

Sanarwar ta zargi El-Rufai da kokarin karkatar da hankalin jama’a daga binciken da Majalisar ke yi, ta hanyar yada bayanai marasa tushe.

Sai dai Majalisar ta ce duk da wadannan zarge-zarge, tana nan daram a kan aikinta na doka da kuma tallafawa Gwamna Uba Sani domin ci gaban Jihar Kaduna.

Majalisar ta jaddada hadin kan mambobinta, tana mai cewa duk da bambance-bambancen siyasa, a shirye suke su ci gaba da aiki domin ci gaban Kaduna da jin dadin al’ummarta.

Copyright © 2024 kaduna Reports.