Gwamnan jihar Kaduna, Mai Girma Sanata Dakta Uba Sani, ya amince da naɗa sabbin mambobi biyu domin yin aiki a cikin Komitin musamman na aikin hajj.
Bayani hakan na kunshen ne a cikin wani sanarwa da Ibraheem Musa, Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna ya fitar a ranar 19 ga Fabrairu, 2025.
Sabin membobin kominti sun hada da Halliru Abdullahi Maraya da kuma Abdullahi Bayero.
Yayin da yake taya su murna, Gwamna Uba Sani ya bukaci sabbin mambobin da su yi aiki da kwarewa, gaskiya da rikon amana. Ya yi musu fatan samun jagorancin Allah a wannan sabon aiki da aka ɗora musu.
TAKAITACEN BAYANI GAME DA SABIN MEMBOBIN
Halliru Abdullahi Maraya
Halliru Abdullahi Maraya ƙwararre ne a harkokin addinin Islama, mai fafutukar zaman lafiya da kuma haɓaka tattaunawar addinai. Ya taɓa zama mai ba da shawara na musamman ga hwamnan jihar Kaduna daga 2011 zuwa 2015, sannan kuma babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kaduna kan harkokin addinin m usulunci daga 2010 zuwa 2011. Hakazalika, ya kasance Ko’odinetan Arewa na Global Peace Foundation, Nigeria. Yanzu haka, shi memba ne a Kwamitin Ƙasa na Ulama kan Hajj.
Halliru Maraya yana da kwarewa a sulhu, tattaunawar addinai, shugabanci da kuma gudanarwa. Shi ne ɗaya daga cikin waɗanda suka lashe kyautar Global Peace Foundation Award for Interfaith Actors a shekarar 2017.
Abdullahi Bayero
Abdullahi Bayero gogaggen ɗan kasuwa ne, masani a harkokin gwamnati, kwararre a dabarun sadarwa, kuma mai rajin kare haƙƙin marasa galihu.
A shekarar 2015, ya kasance mataimakin gwamnan jihar Kaduna na musamman kan harkokin hulɗa da jama’a. A shekarar 2024, ya yi aiki da hukumar hajj ta kasa (NAHCON) a matsayin mai sa ido kan harkokin gudanarwa, inda ya jagoranci daidaita harkokin tafiya, sufuri, da walwalar alhazai. A shekarar 2019, ya kasance memba a kwamitin ulama na hukumar hajj ta kasa. Sannan a shekarar 2017, ya kasance memba a kwamitin abinci na hukumar hajj ta kasa.
Abdullahi Bayero yana da digiri na biyu (Masters) a fannin Kasuwanci (Business Administration) da kuma difloma ta gaba da digiri (Postgraduate Diploma) a fannin Gudanarwa (Management).