Connect with us

Labarai

Kwamishinan Lafiya Ta Yabi Kudurin Gwamna Uba Sani na Karfafa Ma’aikatan Lafiya a Jihar Kaduna

Published

on

Kwamishinan lafiya, Hajiya Umma K. Ahmed, ta yabawa jajircewar mai girma Sanata Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna, wajen inganta ma’aikatan lafiya.

Ta bayyana hakan ne a yayin wani taron bita na kwanaki biyar da aka shirya domin tsara shirin dabarun kula da ma’aikatan lafiya na jihar.

Taron wanda yake gudana a Tahir Guest Palace, Kano, an shirya shi ne domin samar da shirin dabarun kula da ma’aikatan lafiya na shekarar 2025 zuwa 2030 da cikakken tsari da kudade.

Hajiya Umma ta jaddada cewa amincewar Gwamna Uba Sani da manufar kula da ma’aikatan lafiya ya bukaci samar da cikakken shirin dabaru domin aiwatar da manufar yadda ya kamata.

Ta bayyana cewa wannan shirin zai zama taswirar warware matsalolin da suka shafi karancin ma’aikata, gina kwarewa, rarrabuwar ma’aikata cikin adalci, da kuma dorewar su a fannin lafiya.

Yayin da take jawabi ga mambobin Technical Working Group (TWG) da mahalarta taron, Hajiya Umma ta bukaci cikakken gudunmawarsu, tana mai cewa shawarwarinsu za su taka muhimmiyar rawa wajen tsara wannan muhimmin takardu wanda ba kawai zai magance matsalolin gaggawa ba, har ma zai tabbatar da dorewar kulawa da ingancin ma’aikatan lafiya.

Bugu da ƙari, kwamishinan ta jinjinawa goyon bayan abokan huldar gwamnati kamar shirin Lafiya, WHO, da HSDF saboda gudunmawar su ta fasaha, tallafin kuɗi, da kuma jajircewarsu wajen samar da ingantaccen sashen lafiya mai ɗauke da isassun kayan aiki.

Copyright © 2024 kaduna Reports.