Connect with us

Labarai

ASUU-KASU: Jami’ar Jihar Kaduna Ta Tsunduma Yajin Aiki

Published

on

Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen jami’ar jihar Kaduna (KASU), ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a ranar talata sakamakon matsalolin jin daɗin ma’aikata da ba a warware ba.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Peter Adamu, da sakataren kungiyar, Peter Waziri, suka fitar a ranar Talata.

A cewar sanarwar, wannan mataki na yajin aiki ya samu amincewar majalisar zartarwa ta ASUU na kasa, inda aka bayyana cewa yajin aikin zai kasance cikakke, ba tare da wani sassauci ba, kuma na sai baba-ta-gani.

Sanarwar ta kuma kara da cewa kungiyar ta yi watsi da alkawuran da gwamnatin jihar Kaduna ta yi, saboda rashin cikakken bayani, bayyananniyar hanya, da kuma jadawalin biyan hakkokin da ake bin ta.

Kungiyar ta bayyana cewa rashin biyan albashin da aka dakatar wa ma’aikata na daga cikin matsalolin da suka haddasa yajin aikin.

Sauran matsalolin da ba a warware ba sun hada da rashin biyan alawus na Academic Earned Allowances daga shekarar 2016 zuwa yau, biyan kudaden karin girma, da kuma kudaden kula da dalibai a karkashin shirin Students’ Industrial Work Experience Scheme (SIWES).

Haka kuma, rashin biyan inshorar rayuwa ga mambobi da suka rasu, rashin biyan fansho daga shekarar 2009 zuwa 2019, da kuma aiwatar da karin albashi na kashi 25 da 35 cikin 100, na daga cikin matsalolin da ba a magance ba.

Har ila yau, kungiyar ta bukaci a mayar da ‘yancin gudanar da jami’ar ba tare da tsoma bakin gwamnati ba.

Copyright © 2024 kaduna Reports.