Connect with us

Labarai

Gwamnati Taraya Ta Mika Ma Jihar Kaduna Mutum 59 Da a Ka Yi Garkuwa Dasu

Published

on

Nuhu Ribadu/x

Gwamnati taraya ta karkashin ofishin mai ba ma shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ta mika ma gwamnati jihar Kaduna mutum 59 da a ka kubatar da ga hanun masu garkuwa da mutane.

Sani Kila, Wanda ya wakilci mai girma gwamna jihar Kaduna Sen. Uba Sani, ya mika godiya ga Ribadu nagani cewa duk wanda akayi garkuwa da su sun kubuta kuma sun koma cikin iyalansu.

Cikin mutane da aka mika sun hada da maza guda 24 mata 28 da yara guda 6, yayin da guda 1 yake asibiti inda ake duba lafiyar sa.

Wanna nasara ta samu ne a dalilin hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro a kan umarni shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu.

Ribadu ya kara da yaba ma gwamnati jihar Kaduna na bada hadin kai da goyon bayan gwamnati taraya da jami’an tsaro.

Copyright © 2024 kaduna Reports.