Gwamna jahar Kaduna, Sen. Uba Sani, ya kadamar da talafin kayan aiki noman rani ga manoman jihar Kaduna.
Bikin Wanda ya gudana a dandalin Murtala dake cikin birnin Kaduna a ranar lahadi.
Haka zalika taron ya samu halarcin minista noma na kasa Sanata Aliyu Sabi Abdullahi.
A yayin jawabin sa ministan ya bayana jahar Kaduna a matsayin cibiyar jahohin arewacin Nijeria, ya kuma kara da yabon gwamnati Uba Sani kan yadda ta bai wa harkan noma mahimanci ta hanya kara ma ta kasafin kudi.
Har ila yau, yakara da kiran kan kula kawance tsakanin gwamnati Jihar Kaduna da kuma ma’aikatar noma na tarayya tare da kira ga manoma da su yi anfani da kayayakin da aka basuta hanyar da ya dace.
Kayayakin da aka raba sun hada da buhu taki guda dubu dari, injina ban ruwa na zamani dake aiki da solar da ya kai dubu goma ta re da maganin kwari dubu biyu da wasu kayayakin noma.