Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

ICAN ta karrama Gwamna Uba Sani da lambar yabo ta kwarewa a Legas

Published

on

Cikin wata gagarumar taro da ke cike da yabo da karramawa, ICAN ta ba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, lambar yabo ta kwarewa, duk da cewa ba dan kungiyar bane.

An gabatar da lambar yabon ce a jiya da daddare, yayin bikin cin abincin dare da bayar da lambar yabo na shekara-shekara na ICAN, wanda aka gudanar a cibiyar taro ta Monarch da ke Lekki, Jihar Legas.

Wannan lamba ta musamman tana karkashin rukunin “Wanda Ba Dan Kungiya Ba” – wato ana baiwa wadanda ba ‘yan ICAN ba, amma suka taka muhimmiyar rawa wajen inganta aikin kudi da goyon bayan gaskiya da nagarta a harkokin mulki.

Sanata Uba Sani ya samu wannan yabo ne bisa kyakkyawan jagoranci da goyon bayan da yake baiwa harkokin gaskiya da daidaito a cikin gwamnatin jihar Kaduna.

Mataimakiyar Gwamna ta Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ce ta karbi lambar a madadin Gwamnan. Ta samu rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati ciki har da Akanta Janar na Jihar Kaduna, Bashir Zuntu; Kwamishina mai kula da jin dadin al’umma, Rabi Salisu; da Sakatarenta na musamman, Hafsat Aminu Ashiru.

Taron ya tattaro shugabanni, masu tsara manufofi da kwararru daga sassa daban-daban na kasar cikin wani kyakkyawan yanayi na karramawa da tunawa da nagarta.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.