Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

EFCC ta kama wani dan kwangila a Kaduna kan zargin damfara

Published

on

Hukumar EFCC ta kama Bashir Bello Ibrahim a Kaduna bisa zargin damfarar naira biliyan 30.

Shi ne shugaban kamfanin Formal Act Legacy Ltd. kuma ya taba aiki da gwamnatin jihar.

EFCC ta ce yana ikirarin yana da yarjejeniya da gwamnati da wasu kungiyoyi masu alaka da SDGs, duk da cewa an soke yarjejeniyar tun shekarar 2023.

Ana zarginsa da karbar kayan aiki kamar magunguna, gadon asibiti da injinan famfo, yana cewa don ayyukan gwamnati ne.

Amma maimakon ya kai su inda ya dace, sai ya boye su, wasu kuma ya sayar.

An gano kayayyaki da dama a hannunsa ciki har da mota, magunguna, da kayan asibiti.

NAFDAC da Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kaduna sun ce wasu daga cikin magungunan sun kare wa’adinsu, wasu kuma ba su da rajista.

EFCC ta ce za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.