Jam’iyyar APC a karamar hukumar Sanga ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani domin tsayawa takara a zaben 2027.
Wannan na zuwa ne bayan wani taron jam’iyyar da aka gudanar a Gwantu, inda manyan jiga-jigan gwamnati suka halarta, ciki har da mataimakiyar gwamna, Dr. Hadiza Balarabe; Hon. Ado Dogo; dan majalisa Hon. Gambo Dangana; da shugaban Sanga, Anto Usman.
Dr. Balarabe ta yaba da yadda gwamnatin Uba Sani ke sauya rayuwar jama’a, musamman da aikin titin Sanga-Jema’a da gwamnati ta fara. Ta bukaci mambobin jam’iyyar su hada kai domin cigaban APC.
Shugaban karamar hukumar, Anto Usman, ya ce mutanen Sanga za su mara wa gwamnan baya saboda irin ayyukan raya kasa da ya kawo musu.
Jam’iyyar ta ce hadin kai da cigaba na zamani ne ke jan ra’ayinsu wajen marawa shugabannin biyu baya.