Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

ASUU-KASU ta nesanta kanta daga dakatar da yajin aikin da jami’ar Kaduna ta sanar

Published

on

Kungiyar malaman jami’oi ASUU reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta bayyana cewa sanarwar da shugaban jami’ar, Farfesa Abdullahi Musa, ya yi kan dakatar da yajin aikin kungiyar ba ta da tushe balle makama.

A wata takarda da shugabannin ASUU-KASU suka fitar ranar Alhamis, kungiyar ta ce ba shugabancin jami’ar ne suka kira yajin aikin ba, don haka ba ta da hurumin dakatar da shi.

Takardar, wadda shugaban rikon kwarya na ASUU-KASU, Comr. Abubakar Abdullahi da sakataren kungiyar, Comr. Peter Waziri, suka sanya wa hannu, ta bayyana cewa har yanzu kungiyar na jiran Bayanai daga (NEC) dangane da matakin da aka cimma a taron gaggawa da aka gudanar a ranar 15 ga Mayu, 2025.

ASUU-KASU ta shawarci jama’a da su yi watsi da sanarwar da aka ce jami’ar ta fitar, tana mai jaddada cewa dakatar da yajin aiki ba zai yiwu ba sai da umarnin uwar kungiyar ta kasa.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.