Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kaddamar da masana’antar sarrafa lithium ta farko a Najeriya.
Masana’antar, wadda ke Kangimi kan hanyar Kaduna-Jos, za ta rika sarrafa ma’adinan lithium fiye da ton 30,000 a rana.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Kasa, Abubakar Buba, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a gidan gwamnatin jihar.
Wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin jihar na bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da kuma dakile hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Gwamnatin ta ce wannan masana’anta na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin kara janyo masu zuba jari da kuma samar da ayyukan yi ga matasa a fadin jihar.