An fara gudanar da taron duba yadda aka cimma kudaden shiga da aka tsara na watanni ukun farko na shekarar 2025 a Jihar Kaduna.
Taron ya gudana ne a zauren taro na Hukumar Tsare-tsare da Kasafin Kudi, karkashin jagorancin Kwamishinan Hukumar, Hon. Mukhtar Ahmad Monrovia.
A cikin mahalarta taron akwai Akanta Janar na Jihar Kaduna, Hon. Bashir Suleiman, wakilin Shugaban Hukumar Kula da Haraji ta Kaduna (KADIRS), Sakatare kuma mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Barrister Aysha Ahmad Muhammad, da wasu daraktoci daga sassan gwamnati daban-daban.
Manufar taron ita ce duba yadda kowace ma’aikata ko hukuma da ke da alhakin tara kudaden shiga ta samu nasarar cika abin da aka tsara, da kuma tantance matsalolin da suka kunno kai a aikin.