Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Hon. Larai Sylvia Ishaku Ta Ziyartar Ramindop Bayan Iska Mai Karfi Ta Lalata Gidaje

Published

on

Shugabar Karamar Hukumar Jaba, Hon. Larai Sylvia Ishaku, ta kai ziyara zuwa kauyen Ramindop a ranar Laraba bayan wata iska mai ƙarfi tayi sanadiyar lalata gidaje da dama a yankin.

Iskar ta rushe gidaje da dama, inda wasu iyalai suka rasa mafaka. Hon. Ishaku ta yi alƙawarin tuntuɓar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA) domin bada kayan agaji ga waɗanda abin ya shafa.

Shugabar ta tabo batun sauyin yanayi, inda ta yi kira ga al’umma da su taimaka wajen rage mummunan tasirin sauyin yanayi ta hanyar shuka itatuwa da sauran hanyoyin kare muhalli domin rage hatsarin da sauyin yanayi ke haifarwa.

Shugaban kauyen Ramindop, wanda ya wakilci al’umma, ya gode wa Hon. Ishaku bisa wannan ziyara. Ya ce hakan ya nuna shugabanci na gaskiya da ke sauraron koke-koken jama’a

Babban abin godiya shi ne babu rai da ya salwanta a lokacin ibtila’in.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.