Hukumar Tsara Birane da Raya Garuruwa ta Jihar Kaduna (KASUPDA) ta ƙaddamar da sabon shafin yanar gizo mai suna www.kasupdapermit.com, domin sauƙaƙa harkokin neman lasisin gine-gine a fadin jihar.
Fasahar zamani an kirkire shi ne karkashin jagorancin Daraktan Janar na KASUPDA, Bldr. Dr. Abdurrahman Yahya, wanda ke ci gaba da inganta ayyukan hukumar ta hanyar amfani da fasahar zamani.
A cikin jawabin sa, DG ya jaddada cewa, “Duk wannan ci gaba da kirkire-kirkire sun samu ne saboda goyon baya da kwarin gwiwa daga ubangidana, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.”
Yanzu haka, ba sai ka je ofishin KASUPDA ba — zaka iya gudanar da duk wata bukata ta lasisin gini daga gida, ko daga gado.
Sabon tsarin zai ba jama’a damar yin muhimman ayyuka na gine-gine cikin sauki kamar:
Sabunta lasisin gini cikin sauki daga gida.
Bibiya da tabbatar da biyan kuɗi.
Samun bayani na ainihi kan matsayin aikin gine-gine.