Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bukaci Alhazai 4,062 da ke shirin tafiya Hajji daga jihar da su zama wakilai Kaduna da Najeriya na gari a Saudiyya.
An bayyana hakan ne ta bakin mataimakiyar gwamna, Dakta Hadiza Balarabe, yayin kaddamar da jigilar farko na alhazan daga filin jirgin sama na Kaduna.
An nada Sarkin Kauru, Alhaji Ya’u Shehu Usman, ne Amirul Hajj na bana, domin kula da sauran jami’an aikin hajjin don samar da kula, jindadi da walwalar Alhazai jihar a kasa me tsarki.
Uwargidan gwamna, Hajiya Hafsat Uba Sani, ta shawarci Alhazai su bi umarnin malamai domin samun hajji mai karbuwa.
Jigilar farko da suka tashi sun hada da maniyata daga karamar hukumar Giwa da kuma yan hedikwatar hukumar hajji.