Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Gwamnatin Kaduna Ta Sake Jaddada Hadin Gwiwa Tsakanin Ta Da NNDC

Published

on

Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta karbi bakuncin shugabannin kamfanin cigaban Arewa, wato New Nigerian Development Company (NNDC), a yau Litinin, a fadar gwamnatin jihar dake Sir Kashim Ibrahim House, Kaduna.

Shugaban hukumar gudanarwar NNDC, Alhaji Lamis Shehu Dikko, ne ya jagoranci tawagar. A yayin ziyarar ban girma, Alhaji Dikko ya nuna godiyarsa ga Gwamnatin Jihar Kaduna bisa goyon bayan da take bai wa kamfanin, tare da yabawa dangantakar kut-da-kut da ke tsakanin su tun tsawon shekaru.

Ya kuma jinjinawa Gwamna Sanata Uba Sani bisa irin tallafi da jagoranci da yake bai wa yunkurin gyara da bunkasa NNDC domin samun tasiri mai zurfi a fannin ci gaba da raya kasa.

Alhaji Dikko ya jaddada cewa bikin dasa harsashin ginin Special Agro-Processing Zone (SAPZ) da aka yi a Kaduna kwanan nan, wata babbar nasara ce da za ta taimaka wajen inganta samar da abinci, bunkasa harkokin noma, da karfafa tattalin arzikin yankin Arewa.

A nata jawabin, Dakta Hadiza Balarabe ta yaba da hangen nesa na sabon tsarin NNDC, inda ta tabbatar da cikakken goyon bayan Gwamnatin Kaduna a kokarin kamfanin na samar da ci gaba mai dorewa.

Tawagar ta NNDC ta hadu da manyan jami’an gwamnati a lokacin ziyarar, ciki har da Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna, Dakta Abdulkadir Mu’azu Meyere.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.