A yau ne aka gudanar da taron karo na uku na kwamitin dabarun bunkasa jarin dan adam da zuba jari na zamantakewa a jihar Kaduna, karkashin jagorancin Mataimakiyar Gwamnan jihar, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe.
Taron ya gudana a zauren taro na Mataimakiyar Gwamna da ke fadar gwamnati, Sir Kashim Ibrahim House.
An tattauna dabarun fadada shirye-shiryen tallafin gwamnati da nufin kai su ga al’umma da ba su da saukin samu, musamman a karkara da yankunan da ke bukatar kulawa ta musamman.
Mataimakiyar Gwamna Dr. Hadiza Balarabe ta jaddada kudirin gwamnatin jihar na ci gaba da inganta rayuwar al’umma ta hanyar zuba jari a bangaren lafiya, ilimi, abinci, da walwala.
Taron ya nuna yadda gwamnatin Uba Sani ke daukar cigaban jarin dan adam da matakin farko wajen gina jihar da kuma tabbatar da ci gaban da zai dore har abada.
Wannan taro na uku na daga cikin jerin kokarin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi domin tabbatar da adalci da daidaito wajen raba albarkatu da inganta rayuwar al’umma, musamman matasa, mata da marasa galihu.