Gwamna Uba Sani Na Karbar Taron Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna yana karbar taron Gwamnonin Jihohin Arewa da Sarakunan Gargajiya na yankin, wanda ke gudana a fadar gwamnatin jihar, Sir Kashim Ibrahim House, Kaduna.
Taron yana karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, wanda shi ne shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, shi ne ke jagorantar tawagar Sarakunan Gargajiya daga jihohin Arewa.
Manufar taron ita ce tattauna matsalolin tsaro, tattalin arziki da hadin gwiwar Arewa wajen ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani yayin da taron ke gudana.