Hon. Munira Suleiman Tanimu, Shugabar Masu Rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ta gudanar da wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki a gidan ta da ke Saminaka.
Taron ya samu halartar manyan mutane daga mazabar Lere ta Gabas don tattauna batutuwan da suka shafi al’umma da jam’iyyar (APC).
Bayani taron na kunshe ne a cikin sanarwa da Mai Taimaka Mata kan Harkokin Yada Labarai, Ibrahim Munir, ya fitar a dandalin sada zumunta a ranar laraba.
A gurin taron, Hon. Munira ta jaddada goyon bayanta ga jami’ar APC, al’ummar Lere ta Gabas da kuma Gwamna Malam Uba Sani.
A cikin jawabin ta, Hon. Munira ta yi kira domin samun ci gaba da hadin kai da kuma yin aiki tare tsakanin shugabanin da aka zaba da kuma mutanen da ake wakilta.
Ta kuma tabbatar da jajircewar ta wajen aiki tare da masu ruwa da tsaki don inganta ci gaban Lere ta Gabas da jihar Kaduna baki daya.
“Hadinkai da kuma gudunmawar al’umma suna da matukar muhimmanci wajen samun cigaba mai dorewa,” in ji Hon. Munira. “Dole ne mu hada kai don tabbatar da ci gaban mazabar mu da jihar mu baki daya.”
A karshe, Hon. Munira ta sake tabbatar da nufin ta na ci gaba da aiki tukuru don kawo cigaba a Lere ta Gabas, Karamar Hukumar Lere, da jihar Kaduna.