Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Nuhu Bamalli Polytechnic Ta Karrama Tsoffin Ma’aikata Makarantar

Published

on

Hukumar makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic, Zariya ta karrama wasu daga cikin tsoffin ma’aikatan da suka taka rawar gani ci gaban makarantar tun daga zamanin KCAST har zuwa yanzu.

Taron karamawar ya gudana ne a harabar makarantar karkashin jagorancin Rector, Injiniya Dr. Mohammed Kabir Abdullahi, inda aka bayyana lambobin girmamawa ga tsoffin shugabanni da malamai da suka sadaukar da rayuwarsu wajen bunkasa harkar ilimi a jihar Kaduna.

“Mun zo ne domin tunawa da irin gudunmawar da wadannan manya suka bayar wajen gina Nuhu Bamalli Polytechnic. Ba za mu manta da su ba,” cewar Rector yayin jawabi.

A cikin wadanda aka karrama akwai fitattun shugabanni na kasa da suka taba aiki da makarantar. Sun hada da: Rt. Hon. Abbas Tajuddeen, Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Balarabe Abbas Lawal, Ministan Muhalli, Alhaji Musa Daji Abdullahi MFR, Alhaji Salisu Halidu MNI, Injiniya Aminu Aliyu, Malam Suleiman Lawal Kauru Jarman Kauru, Arc. Mohammed Aminu Idris MNI, Hakimin Rigasa.

Sauran sun hada da jami’an gwamnati, malamai, da iyalan wadanda aka karrama bayan rasuwarsu kamar Marigayi Aliyu Mohammed Shika.

Rector ya yaba da kokarin Gwamnan Jihar Kaduna, Sen. Dr. Uba Sani, bisa ayyukan ci gaba da ake gudanarwa a makarantar, musamman rage kudin makaranta.

“Wannan sauki da gwamnatin jiha ta kawo ga dalibai ya nuna cewa gwamnati na da niyyar bunkasa ilimi mai inganci,” in ji shi.

Alhaji Musa Daji Abdullahi, wanda shi ne shugaban taron, ya wakilci wadanda aka karrama. Ya bayyana godiya ga hukumar makarantar bisa wannan karramawa da kuma cigaban da makarantar ke samu.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.