Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa jita-jitar da ke yawo game da fashewar bam a unguwar Josawa Road, Abakpa, karamar hukumar Kaduna ta arewa, ba gaskiya ba ce kuma an yi wuce gona da iri wajen yada jita-jitar.
A cewar sanarwar da kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida, Sir James A. Kanyip, ya fitar, a ranar laraba.
Kanyip, ya bayana cewa abin da ya faru a ranar talata 22 ga Afrilu, 2025, ba fashewar bam ba ne, illa fashewar bindiga kirar gida (dane gun) da ta tashi ba da gangan ba.
Yaro Daya Ya Rasu, Wasu Bakwai Sun Jikkata
A cikin lamarin, wani yaro dan shekara 12 ya rasa ransa, yayin da wasu mutum bakwai suka jikkata sakamakon fashewar bindigar. Wannan ne ya janyo firgici da rudani a tsakanin mazauna yankin, wanda ya haddasa yaduwar jita-jitar karya.
Hukumar ‘Yan Sanda da DSS Sun Tabbatar da Hakikanin Lamarin
Kwamitin tsaro da ya kunshi ‘yan sanda, DSS, sojojin Najeriya, da shugaban karamar hukumar Kaduna North, sun ziyarci wurin da lamarin ya faru don tabbatar da gaskiyar al’amari. Sun tabbatar da cewa ba bama-bamai aka tarwatsa ba, kuma ba wani hari na ta’addanci da aka kai a unguwar ba.
Gwamnati Na Ci Gaba da Bincike, Jama’a Su Zauna Lafiya
Kwamishina Kanyip ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma gwamnatin jihar tana tabbatar wa da al’umma cewa an dauki matakan tsaro don kare rayuka da dukiyoyinsu. Ya bukaci jama’a su cigaba da gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali, tare da gujewa yada jita-jita marasa tushe.