Gwamnatin Jihar Kaduna ta soke duk wata sayar da gidajen da ke cikin manyan makarantun masu tarihi a fadin jihar Kaduna, domin kare muradun jama’a da samar da ingantaccen yanayi na koyarwa da koyon illimi.
Gidajen da aka soke sayar wan su, sun hada da gidajen dake cikin Harabar makarantar Kwalejin Alhuda-Huda dake Zaria, Kwalejin Queen Amina dake Kaduna da kuma Kwalejin Government Commercial dake Zaria.
Sanarwar soke siyar da gidajen ya fito ne daga Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna, Dr. AbdulKadir Mu’azu Meyere, inda ya ce an riga an tura umarnin soke siyar da gidajen ga wadanda suka mallake gidajen, kuma tuni an fara shirye-shiryen mayar musu da kudaden da suka biya.
Matakin yana da nasaba da manufofin Gwamna Uba Sani na bunkasa ilimi da ci gaban dan Adam (Human Capital Development). A cewar Gwamna Uba Sani: “Ilimi ba wai kawai yana daidaita bambance-bambance da ke tsakanin mutane ba ne, har ma yana zama hanya mafi tasiri wajen sauya rayuwar al’umma da inganta walwalarsu.”
Gwamnati na fatan hakan zai inganta yanayin koyarwa da kuma hana wani abu da zai hana ci gaban makarantu.