Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Rt. Hon. Abbas Tajuddeen, GCON, ya kaddamar da babban shirin tallafa wa jama’a a Zariya da yankin Zone One na Jihar Kaduna, inda ya raba motoci 100, keke Napep 500, da babura 1,000 ga masu bukata.
An gudanar da taron bada tallafin ne a Filin Wasan Kwallon Kafa na Nasara, Kofar Doka, Zariya, inda dubban jama’a suka halarta domin karɓar kayan aikin.
Rt. Hon. Abbas ya bayyana cewa wannan shiri wani bangare ne na kokarinsa na: Samar da ayyukan yi, Taimakawa matasa da ’yan kasuwa kanana Inganta harkar sufuri da zirga-zirga a cikin gari.
Gwamna Uba Sani Ya Yaba
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Dr. Uba Sani, wanda ya kasance Babban Bako na Musamman, ya jinjinawa Kakakin Majalisar bisa yadda yake damuwa da talakawa da ci gaban matasa a matakin tushe.
Ya ce irin wannan shiri zai taimaka wajen rage zaman banza da talauci a cikin al’umma.
Jama’a Da Shugabanni Sun Nuna Goyon Baya
Taron ya samu halartar manyan shugabanni na siyasa, sarakunan gargajiya, da dimbin jama’a. Dukkanin su sun bayyana shirin a matsayin na lokaci kuma mai amfani ga al’umma.
Wannan tallafi yana cikin hangen nesa na Rt. Hon. Abbas Tajuddeen na gina tattalin arziki mai dorewa, ta hanyar tallafa wa iyalai da matasa da ke bukatar jari ko hanyar samun kudin shiga.