Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

Gwamnatin Kaduna Ta Fitar da Sunayen Masu Cin Gajiyar Fansho: Naira Biliyan 3.8 Da Za a Biya

Published

on

Hukumar Fansho ta Jihar Kaduna ta fitar da jerin sunayen wadanda za su ci gajiyar biyan fansho, hakkokin mutuwa, da kuma hakkokin da suka taru tun kafin zuwan sabuwar tsarin fansho (accrued rights), duka daga matakin jiha da kuma kananan hukumomi.

Wannan mataki na zuwa ne bayan amincewar Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da sakin Naira biliyan 3.8 domin biyan wadannan hakkoki.

Ga Sharuddan Da Ake Bukata Domin Tabbatar Da Biya: Ga Masu Ritaya (Retirement Benefit):

  1. Takardar bayanin asusun fansho na shekara guda daga banki (daga Afrilu 2024 zuwa yau).
  2. Takardar BVN daga banki.
  3. Asalin da kwafi uku na takardar lissafin hakkoki (computation sheet).
  4. Hoton fasfo guda biyu.
  5. Asalin da kwafi guda na takardar tabbatar da daukar aiki (Confirmation of Appointment).
  6. Asalin da kwafi guda na takardar amincewar ritaya (Approval of Retirement).
  7. Asalin da kwafi guda na katin shaida na kasa (National ID).

Ga Hakkin Mutuwa (Death Benefit):

Takardun asalin wanda ya rasu da suka shafi aikinsa a matakin jiha ko karamar hukuma.

2. Asalin bayanin asusun banki na marigayin daga shekara biyu kafin ya rasu zuwa biyu bayan rasuwarsa.

3. Asalin da kwafi uku na wasikar kula da gadon marigayi (Letter of Administration).

4. Asalin da kwafi biyu na bayanin asusun gado (Estate Account).

5. Takardar tabbatar da bude asusun gado daga banki.

6. Asalin da kwafi uku na takardar lissafin hakkokin marigayin.

7. Hoton fasfo guda biyu na ’yan gado (next of kin).

8. Asalin da kwafi guda na wata shaida ta ’yan gado (ID card, katin zabe, fasfo, ko lasisin mota).

9. Hoto na marigayin.

10. Takardar shaidar mutuwa (Death Certificate).

Lura: Ana bukatar cika wadannan sharudda duka kafin a amince da biyan kowane hakki.

Wannan mataki yana cikin kokarin gwamnati na tabbatar da adalci da jin kai ga tsofaffin ma’aikata da iyalan wadanda suka rasu.

Gwamnatin Uba Sani na ci gaba da tabbatar da ganin cewa kowane dan jihar Kaduna yana da kwanciyar hankali bayan ritaya ko rasa masoyi.

Copyright © 2024 kaduna Reports.