Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Siyasa

2027: Jiga-Jigan Jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Chikun Sun Bayyana Goyon Bayan su Ga Shugaba Tinubu da Gwamna Uba Sani Domin Tazarce

Published

on

Jiga-jigan jam’iyyar APC a karamar hukumar Chikun sun gudanar da muhimmin taro domin nuna cikakken goyon bayan su ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani domin sake tsayawa takara a zaben shekarar 2027.

A cewar jagororin jam’iyyar, cikin shekara daya da watanni goma sha daya, gwamnatin mai ci ta nuna bajinta a fannoni daban-daban na shugabanci, inda aka samu gaskiya, rikon amana da hadin kai tsakanin matakan gwamnati.

“Gwamna Uba Sani yana tafiyar da gwamnati mai hada kowa da kowa, kuma a yau a jihar Kaduna muna morewa zaman lafiya da raguwar matsalolin tsaro da suka dabaibaye yankunanmu a baya,” in ji daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar.

Gwamnatin Kaduna karkashin Uba Sani ta zage damtse wajen inganta noma, raya karkara, gine-ginen ababen more rayuwa, da ci gaba a fannin ilimi da tsaro.

“Mun ga ayyuka da suke magana da kansu – hakan ya tabbatar mana cewa mun zabi shugabanni na gari. Ba tare da wata-wata ba, mun bayyana goyon bayan mu na gaskiya ga Tinubu da Uba Sani don ci gaba a 2027.”

A yayin kammala taron, jiga-jigan jam’iyyar sun bukaci ‘yan jam’iyya da kungiyoyin goyon baya da su: Fadada wayar da kai a matakin tushe (grassroot mobilisation), inganta hadin kai tsakanin mambobi, kiran masu ra’ayin daban zuwa ga fahimta tare da goyon baya.

Wannan mataki na nuna goyon baya a karamar hukumar Chikun na nuni da karfin jam’iyyar APC da kuma amincewar al’umma da tafiyar Tinubu da Uba Sani a matakin kasa da jiha.

Copyright © 2024 kaduna Reports.