Hukumar KASTELEA za ta kashe naira miliyan 48 gun maida motocin aikin ta zuwa CNG daga anfani da man fetur a shekarar 2025.
Bayanin kashe kudin na kunshe ne acikin kasafin kudi na shekarar 2025 na jihar Kaduna, a karkashin kasafin hukumar ta KASTELEA.
A kasafin na shekarar 2025, an bayana kashe kudin sauya motocin aikin hukumar ta KASTELEA daga fetur zuwa CNG a karkashin lambar Admin code: 023400600100 tare da lambar Economic Code : 23050107.
Dukda cewa a shekarar 2025, ana sa rai hukumar ta KASTELEA za ta samar da kudin shiga da adadin sa ya kai kimani naira biliyan 1,667,113,750.